Isa ga babban shafi
Canada

An cafke daruruwan masu zanga-zanga a Canada

‘Yan Sandan Canada sun ce sun cafke Dalibai 400 masu zanga-zangar adawa da karin kudin makaranta a birnin Montreal. An kwashe tsawon watanni Hudu dalibai na zanga-zanga akan karin kudin Jami’ar Quebec.

Arangama tsakanin Jami'an tsaro da Daliban jami'ar Québec masu zanga-zangar adawa da karin kudin makaranta.
Arangama tsakanin Jami'an tsaro da Daliban jami'ar Québec masu zanga-zangar adawa da karin kudin makaranta. REUTERS/Christinne Muschi
Talla

Daruruwan dalibai ne suka fito a saman titunan Birnin Montreal domin zanga-zangar adawa da karin kudin makaranta. Sai dai Jami’an tsaro sun ce Zanga-zangar ta saba doka.

Tun a watan Fabrairu ne Dalibai suke gudanar da zanga-zanga bayan gwamnatin Canada ta kara kudaden Jami’ar Quebec da kashi 82.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.