Isa ga babban shafi
Pakistan

An kashe babban kwamandan Haqqani a Pakistan

Kungiyar Taliban tace wasu ‘Yan bindiga sun kashe Nasiruddin Haqqani a Islamabad, wanda shi ne babban kwamandan kungiyar Haqqani a kasar Pakistan. Taliban tace wasu ‘yan bindiga ne suka buda wuta akan Nasiruddin.

Jalaluddin Haqqani Mahaifin Nasirudden Haqqani da aka kashe a Islamabad
Jalaluddin Haqqani Mahaifin Nasirudden Haqqani da aka kashe a Islamabad AFP PHOTO/str
Talla

A lokacin da ya ke raye, Nasiruddin ya kasance daya daga cikin wadanda Kungiyar tsaro ta NATO karkashin jagorancin Amurka ke zargi da kai hare hare a cikin kasar Afghanistan mai iyaka da Pakistan.

Kisan na shugaban na Haqqani na zuwa ne mako guda bayan hare haren jiragen yakin Amurka sun kashe shugaban Taliban a Pakistan Hakimullah Mehsud a arewacin Waziristan

Wani babban jami’in kungiyar Taliban a kasar Afghanistan ya tabbatarwa Kamfanin Dillacin Labaran Faransa cewa an bindige Nasiruddin ne a yankin Bhara Kahu da ke Islamabad, kuma yace akalla ‘yan bindiga hudu ne suka bude masa wuta.

Yanzu haka Rahotanni sun ce an kwashi gawar Nasiruddin zuwa garin Miranshah babban birnim yankin Waziristan domin yi masa Jana’iza.

A watan Satumba na 2012 ne, gwamnatin Amurka ta jefa sunan Kungiyar Haqqani a cikin  jerin sunayen kungiyoyin ‘Yan ta’adda. Daga nan kuma Majalisar dinkin Duniya ta kakabawa kungiyar Takunkumi akan zargin Haqqani tana da alaka da kungiyar al Qaeda.

Jalaluddin mahaifin Nasiruddin shi ne ya kafa kungiyar Haqqani wanda tsohon Sojan Afghanistan da Amurka ta ba horo domin yaki da dakarun Daular Soviet a kasar Afghnistan a shekarar 1980.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.