Isa ga babban shafi
Yemen

Al Qaeda ta sha alwashin sake kubutar da mabiyanta a Gidan yari

Shugaban kungiyar Al Qaeda reshen kasar Yemen Naser Al-wuhayshi, ya ce nan ba da jimawa ba ne kungiyar za ta ‘yantar da dukkanin magoya bayanta da ke tsare bisa zargin ta’addanci a sassa daban daban na duniya.

Shugaban Kungiyar al Qaeda a yankin kasashen Larabawa Nasser al-Wuhayshi
Shugaban Kungiyar al Qaeda a yankin kasashen Larabawa Nasser al-Wuhayshi AFP/Getty
Talla

A wani sakon bayani da ya yi wa take da “wasika zuwa ga fursunonin da ke hannun azzalumai,’’ shugaban na Al Qeada ya ce, ci gaba da tsare magoya bayansu abu ne da ba zai dauki dogon lokaci ba, kuma za a ‘yantar da su ne ta hanyar farfasa gidajen yarin da ake tsare da su.

Wannan barazana ta zo ne makwanin kadan bayan da magoya bayan kungiyar suka farfasa gidajen yari a kasashen Iraqi da Libya da kuma Pakistan tare da kubutar da mutanen da aka ce manyan ‘yan ta’adda ne.

Wuhayshi wanda ya balle daga gidan yari a shekarar 2007, an bayyana shi a matsayin na hannun damar Marigayi Osama bin Laden.

Kuma a shekarar 2011 ne ya bayyana nuna goyon bayan shi ga shugaban al Qaeda na yanzu Ayman al-Zawahiri.

Gargadin da ke fitowa daga Wuhayshi shi ne ya razana Amurka wanda ya sa ta rufe ofisoshin jekadancinta kafin daga bisani Amurka ta bude ofisoshin a kasashen Larabawa ba tare da bude na Yemen ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.