Isa ga babban shafi
Yemen

Yemen ta yi ikirarin warware wani hari da aka shirya kai wa

Gwamnatin Yemen ta yi ikirarin samun nasarar warware wani hari da kungiyar al Qaeda ta kulla kai wa a wani kamfani hako mai na kasashen waje, a dai dai lokacin da barazanar kungiyar ke razana Amurka da kasashen Turai. Kakakin gwamnatin Yemen Rajeh Badi ya shaidawa kamfanin dillacin labaran Faransa cewa an shirya kai harin ne a wani kamfanin kasar Canada, tare da yukurin yin garkuwa da ma’aikatan kamfanin.

Jami'an tsaro suna aikin samar da tsaro a Sanaa kasar Yemen
Jami'an tsaro suna aikin samar da tsaro a Sanaa kasar Yemen REUTERS/Khaled Abdullah
Talla

Tuni dai Amurka da Birtaniya suka rufe ofisoshin jekadancinsu a birnin Sanaa saboda barazanar da suka ce sun samu ta kaddamar da hare hare daga kungiyar al Qaeda reshen Yemen.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.