Isa ga babban shafi
Najeriya

ASUU - Ba zamu koma aiki ba, ko me gwamnati zata yi

Yau ne wa’adin da gwamnatin tarayyar Najeriya ta gayawa Malaman jami’a a kasar su koma bakin aikinsu ko kuma ta sallame su daga aiki, kamar yanda gwamnatin ta fada

Hatimin Kungiyar ASUU a Nijeriya
Hatimin Kungiyar ASUU a Nijeriya ASUU
Talla

Wannan dai ya zo ne bayan da gwamnatin kasar ta tsawaita wannan wa’adi daga ranar ranar 4 ga wannan wata na Disamba zuwa yau.

To sai dai a cewar shugaban kungiyar Malaman jami’o’in Najeriya da ke yajin aikin da ya share fiye da watanni 4 wato Dakta Nasir Fage, ko a yau ba za su koma aikin ba.

Dakta Nasir Fage ya ce gwamnatin tarayyar Najeriya na manta cewar ba wanda ya isa ya tursasawa Malaman Jami’a a Najeriya, amma zasu zura Ido su ga abin da Gwamnatin zata yi, amma batun komawa aiki kam babu shi.

Dakta Nasir ya ce ya zasu koma aiki ba tare da an yi gyara akan abinda suke kokawa a kai ba, domin idan sun yi hakan, kenan yajin aikin da suka yin a barnar lokaci ne kurum, ba biyan bukata.

Yace ba za su batawa Dalibai da Iyayen su, da sauran ‘yan Najeriya Rayuwa ba, kawai don suna son gwamnatin Najeriya ta morewa biyayyar da zasu yi mata.

Nasir yace dama sun gudanar da taro da shugaban kasa, kuma sun yi musayar bayannai, in gaskiya Gwamnatin Najeriyar ke yi ai sai ta duba bukatun ta kuma cika yarjejeniyar da suka yi.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.