Isa ga babban shafi
Somaliya

Wadanda suka mutu a Bala'in kasar Somaliya ya kai Dari Ukku [300]

Hukumomi a kasar Somaliya sun bayyana samun karin wadanda suka mutu, sakamakon Tsawa da Ambaliyar Ruwa data biyo bayan Ruwan Sama da aka shatata, ya kai akalla mutane Dari Ukku [300]

Ambaliyar Ruwa a kasar Somaliya
Ambaliyar Ruwa a kasar Somaliya sabahionline.com
Talla

Wannan kakkarfan Ruwan Sama da Iska mai karfi da ya ci gaba da kadawa har na tsawon kwanaki a Somaliya, sun tilaswa Hukumomi ayyana Dokar ta-baci bayan fidda Rahotannin da ke cewar akalla mutane Dari Ukku [300] sun mutu.

Sai dai har I zuwa wannan lokaci ba za’a iya tantancewa da yawan mutanen da suka mutu ba, amma kwararru kan Yanayi daga Kungiya kula da ambaliyar Ruwa da Ayukan Gona na Majalisar Dunkin Duniya, sun bayyana cewar ambaliyar Ruwan ta munana ainun.

Masunta da dama dai sun rasa Rayukan su, ko sun bata ba tare da gano inda suke ba, a yayin da kakkarfar Guguwar Ruwa da tsawa suka kacaccala Kauyuka da dama, da Gidaje masu yawa a yankunan Birane, kazalika da manyan gine-gine.

Somaliya dai kasa ce da ta yi ta fama da Bala’o’I tun bayan barkewar yakin basasa da ya tashi sakamakon kifewar Gwamnati a 1991.

A wani labarin kuma Kwamitin Sulhu na Majalisar Dunkin Duniya, ya amince da karin sojojin samar da zaman lafiya Dubu Hudu da Dari Hudu, [4.400] da zasu yi aikin samar da zaman lafiya a kasar ta Somaliya, abinda ya kara yawan Dakarunta, zuwa Dubu Ashirin da Biyu da Dari Daya [22.100] dan fuskantar kungiyar Al-Shebaab.

Daukacin wakilan Kwamitin Goma sha Biyar [15] ne, suka amince da bukatar da kungiyar kasashen Afruka ta gabatar, dan yaki da kungiyar Al-Shebaab mai barazana a kasar.

Yanzu haka sojojin Majalisar Dubu Goma sha Bakwai da Dari Bakwai [17.700] ne, ke aiki  a kasar,  wanda ya nuna karin wasu Dubu Hudu da Dari Hudu [4.400] da zai daga adadin zuwa Dubu Ashirin da Biyu da Dari Dai da Ashirin da Shida [22.126].

Ana saran karin Sojojin da zasu hada da masu kare muradun Majalisar Dunkin Duniya a Mogadishu, su fara isa kasar a farkon shekara mai zuwa.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.