Isa ga babban shafi
Somalia

Za’a sake tura Dakaru 4,000 domin yaki da al Shabaab a Somalia

Wata Majiyar Diflomasiya tace Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya yana dab da amincewa da bukatar aikawa da wasu karin dakaru 4,000 domin taimakawa dakarun Afrika ci gaba da yaki da Mayakan al Shabaab.

Sheikh Muktar Robow Abuu Mansuur daya daga cikin shugabannin kungiyar al Shabaab ta Somalia yana tafiya a birnin Mogadishu dauke da Bindiga
Sheikh Muktar Robow Abuu Mansuur daya daga cikin shugabannin kungiyar al Shabaab ta Somalia yana tafiya a birnin Mogadishu dauke da Bindiga Reuters
Talla

Wannan kudirin kuma, ya biyo bayan barazanar da ke fitowa daga mayakan al Shabaab wadanda suka kai hari a Nairobi inda suka kashe mutane sama da 60.

Mataimakin sakataren Majalisar Dinkin Duniya Jan Eliasson yace akwai bukatar karin dakaru domin taimakawa dakarun Afrika da Somalia da ke yaki da mayakan na al Shabaab.

A watannin da suka gabata, dakarun na Afrika tare da na Somalia sun samu nasarar kora Mayakan al Shabaab daga birnin Mogadishu. Amma hakan be hanawa kungiyar ci gaba da kai hare hare ba musamman harin da suka kai a wata cibiyar kasuwanci a Nairobi kasar Kenya da kuma wani harin kunar bakin wake a Mogadishu.

Kungiyar Tarayyar Afrika ce ta mika bukatar karin dakarun domin fafatawa da mayakan al shabaab a kudancin Somalia. Kuma kudirin zai kai ga samar da wasu dakaru kimanin 4,000 zuwa kasar ta Somalia.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.