Isa ga babban shafi
Kenya-Somalia

An kori sojojin Kenya biyu da aka kama laifin sata a harin Nairobi

Rundunar sojan kasar Kenya ta ce wasu daga cikin jami’anta da aka tura domin fada da ‘yan bindigar da suka kai hari a shagon zamani da ke birnin Nairobi cikin watan jiya, sun yi sata a cikin shagon kuma tuni aka kori sojoji biyu daga aiki.

Wasu daga cikin sojojin Kenya a lokacin da suke arangama da 'yan kungiyar Al Shebab
Wasu daga cikin sojojin Kenya a lokacin da suke arangama da 'yan kungiyar Al Shebab REUTERS/Noor Khamis
Talla

Rundunar tsaron kasar  har ila yau ta tabbatar da zartar da hukuncin dauri a kan wani jami’in tsaro na uku a gidan yari, wadanda aka tabbatar da cewa sun yi sata a cikin wannan kasuwa ta birnin Nairobi.

Shugaban rundunar sojan kasar Janar Julius Karangi, ya bayyana cewa dole ne a hukuntar da wadannan jami’ai da suka aikata laifufukan da ke iya shafa wa jami’an tsaron kashin kaji.

Da farko dai lokacin da ‘yan jaridu suka soma yayata labarin cewa wasu daga cikin jami’an tsaron sun yi sata a lokacin da ake fafatawa da ‘yan bindigar a wannan shago, hukumomin tsaron kasar sun musanta wannan zargi, inda suka ce ba abinda jami'an tsaron suka yi amfani da shi a shagon face ruwan sha.

To sai dai sakamakon yadda aka nuna wani faifan bidiyo da na’urorin daukar hoto a cikin shagon suka nada, wannan ya sa dole rundunar tsaron ta shiga bincike tare da hukunta wadannan jami’ai bayan samunsu da laifi.

A farkon watan da ya gabata ne mayakan Al Shebab suka kai hari a wasu shuganan kasuwanci dake Wastegate a birnin Nairobi, lamari da ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.