Isa ga babban shafi
Jamhuriyyar Congo

Kasashen duniya sun nemi M23 da gwamnatin Congo da su koma tattaunawa

Shugabannin Kasashen Afrika da Majalisar Dinkin Duniya sun bukaci kawo karshen tahsin hankalin da ake a Jamhuriyar Dimokuradiyyar Congo, sannan a ci gaba da tattaunawar zaman lafiyar da ake yi tsakanin bangarorin biyu a kasar Uganda.

Mayakan M23 a Kivu
Mayakan M23 a Kivu RFI/Léa-Lisa Westerhoff
Talla

Kiran dai ya zo ne a daidai lokacin da gwamnatin kasar ta Congo ke ikirarin samun nasarar murkushe ‘yan tawayen wadanda suka jima suna sheke ayarsu a yankin Kivu da ke gabashin kasar.

Shugabar kasar Malawi, Joyce Banda da ke magana da yawun shugabannin kasashen Gabashin Afrika, ta roki bangarorin biyu da su koma teburin shawara, yayin da takwaranta na Uganda, Yuweri Museveni ya ce ya yi mamakin sake barkewar fadan bayan an yi nisa wajen sasanta rikicin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.