Isa ga babban shafi
Jamhuriyyar Congo

Kasashen Afrika sun bude taron nazari akan Congo

Shuganannin kasashen Nahiyar Afrika ke yin taro, don tattauna matakan da za a dauka, wajen aikin samar da zaman lafiya a Jamahuriyar Democradiyyar Congo. Wannan matakin na zuwa ne a daidai lokacin da aka fatattaki ‘Yan tawayen M23 daga yankunan suka mamaye a kasar.

Dakarun Congo sun yi nasarar karbe sansanin 'Yan tawaye a Rumangabo arewacin Goma
Dakarun Congo sun yi nasarar karbe sansanin 'Yan tawaye a Rumangabo arewacin Goma Reuters/Kenny Katombe
Talla

Shugaban Africa ta kudu Jacob Zuma ne zai jagoranci taron na shugabannin kungiyar hadin kan kasashen kudancin Nahiyar ta SADC, da na wasu kasashen da ke makwabta da kasar Congo, a birnin Pretoria.

Kasashen Nahiyar da dama, da suka hada da Afrika ta kudu sun bayar da agajin sojojin da ke aiki karkashin Majalisar Dinkin Duniya, don tallafawa sojan Congo da ke kokarin tursasa wa dakarun na M23 hawa teburin sasantawa.

Mayakan ‘Yan tawayen su kusan 200 aka yi wa kawanya a tsaunukan kasar, da ke da makwabta da Uganda tun ranar Laraba, lokacin da aka karbe sansaninsu da ke garin Bunagana.

A baya Majalisa Dinkin Duniya ta zargi Rwanda da Uganda da ke makwabta da Congo akan suna bayar da tallafi ga ‘Yan tawayen cikin sirri, sai dai kasashen biyu, sun yi ta musanta zargin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.