Isa ga babban shafi
Jamhuriyyar Congo

Dakarun Congo sun kwace garuruwa biyu daga hannun ‘Yan tawaye

Sojojin Jamhuriyar Demokradiyar Congo sun ce sun kama karin garuruwa biyu da suka fada hannun ‘Yan Tawaye, yayin da suka kama hanyar zuwa Rutshuru, a wata alamar samun nasarar dakarun gwamnati. Col Olivier Hamuili, mai Magana da yawun rundunar sojin kasar, yace suna kama hanyar kama garin Rutshuru, amma za su karbi aje makaman wadanda suka bada kai, kuma za su abkawa wadanda suka ki. Yau an shiga rana ta 4 na fafatawar da ake tsakanin sojojin gwamnati da ‘Yan Tawayen.

Dakarun kasar Congo da ke yaki da 'Yan tawayen M23
Dakarun kasar Congo da ke yaki da 'Yan tawayen M23 REUTERS/Kenny Katombe
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.