Isa ga babban shafi
Jamhuriyyar Congo

Dakarun Congo sun kakkabe ‘Yan tawayen M23 a Bunagana

Gwamnatin Kasar Jamhuriyar Demokradiyar Congo, tace sojojinta sun yi nasarar kakkabe ‘Yan Tawayen M23 daga sansaninsu na karshe da ke Bunagana da ke iyakar kasar da Uganda. Ministan yada labaran kasar Lambert Mende, yace yanzu haka garin Bunagana ya koma hannun gwamnatin kasar.

'Yan kasar Congo suna murnar samun nasarar yaki akan 'Yan tawayen M23 da Dakarun kasar suka kakkabe daga yankunan da suka mamaye a kasar.
'Yan kasar Congo suna murnar samun nasarar yaki akan 'Yan tawayen M23 da Dakarun kasar suka kakkabe daga yankunan da suka mamaye a kasar. REUTERS/Kenny Katombe
Talla

Sojojin Congo da ke samun goyan bayan dakarun Majalisar Dinkin Duniya sun yi nasarar korar ‘Yan Tawayen daga yankunan da suke rike da su musamman yankunan arewacin Kivu da suka fada hannun ‘Yan tawayen

Sojin na Congo sun ce tun a ranar Talata ne suka yi wa garin Rutshuru kawanya domin kai farmaki a garin Bunagana da ke kan iyaka da Uganda.

Akalla mutane 5,000 ne suka fice zuwa kasar Uganda domin tsira da rayuwarsu a Congo.

Hukumar kula da ‘Yan gudun Hijira tace adadin mutanen da ke kauracewa yankunan da ake fito na fito tsakanin Dakarun Gwamnati da ‘Yan tawaye ya kai 22,500.

Akwai dai zaman sasantawa da ake yi tsakanin ‘Yan tawayen da gwamnati a kasar Uganda domin cim ma daidaito tsakaninsu.

Amma duk da wannan nasarar har yanzu ‘Yan tawayen M23 barazana ne ga samun zaman lafiya a kasar Jamhuriyar Congo.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.