Isa ga babban shafi
DRC Congo

‘Yan tawayen M23 sun yi kiran tsagaita wuta

Kungiyar ‘Yan Tawayen M23 ta Jamhuriyar Demokradiyar Congo, ta ce tana bukatar tsagaita wuta a yakin da take da sojojin gwamnatin kasar, dan bada damar tattaunawar zaman lafiya.

Wasu daga cikin 'ya kungiyar mayakan M23
Wasu daga cikin 'ya kungiyar mayakan M23 REUTERS/James Akena
Talla

Sanarwar da kungiyar ta bayar ta bukaci masu shirya taron na zaman lafiya a kasar Uganda, da su shirya yadda za su sanya ido kan shirin tsagaita wutar.

Ita dai kungiyar ta M 23 ta kaddamar da hare hare kan dakarun Gwamnati a water Aprilu na shekarar 2012, yakin da ya halalka mutane da dama, kana kuma ya sanya mutane sama da 800,000 suka rasa matsugunan su.

Wannan lamari na aukuwa ne a daidai lokacin da Majalisar Dinkin Duniya ke ikrarin na murkushe daukacin ‘ya’yan kungiyar, inda ta sun fice kungiyar ta fice daga sansanonin da ta kakkafa illa kalilan daga cikinsu.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.