Isa ga babban shafi
DRC Congo

Bukatar MDD na a hukunta sojan kasar Congo

Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci gwamnatin Jamhuriyar Demokradiyar Kongo da ta hukunta wasu sojojin kasar da dama da suka aikata laifufuka daban daban wadanda ke da nasaba da cin zarafin mata a yammancin kasar a shekarar da ta gabata.

AFP PHOTO / SIA KAMBOU
Talla

Shekara daya bayan aukuwar wannan lamari hukumomi a kasar ba su ce upon ba.
Yanzu dai kungiyar kare hakkin bil’adama ta Human right Watch da hadin gwiwar ofishin MDD a a kasar ta kongo sun nemi a gurfanar da sojojin a gaban kotu domin hukunta su.
Gwamnatin a Congo dai ta shiga yarjejeniya da MDD a watan Afrilu na daukar mataki domin yakar laifin cin zarafin mata da kungiyoyin masu makamai, da sojoji ke aikatawa mussaman ma a yankunan da ke fuskantar rikici a yammancin kasar.
Dakarun kasar ta Congo sun dogara ne da amfani da makamai na MDD wajen magance kungiyoyi da ke dauke da makamai da ke wa kasar barazana.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.