Kotun hukunta laifukan yaki ta ICC ta mayarwa shugabannin Afrika da martani
Babbar mai gabatar da kara a kotun hukunta laifukan yaki ta ICC, ta mayar da martani ga zargin da wasu shugabannin Afrika suka yi akan kotun tana nuna wariya a wajen gudanar da ayyukanta.
Wallafawa ranar:
Fatou Bensouda ta ce wadanda suke zargin suna kokarin kare shugabannin da a ke zargi da aikata laifukan yaki ne.
“Duk munsan wadanda ke wannan korari.” Inji Bensouda.
A yanzu haka kotun ta ICC na samun matsain lamba akan tuhumar shugaban kasar Kenya, Uhuru Kenyatta da mataimakinsa, William Ruto bisa zargin keta hakkin bil adama a lokacin da kasar ta fada rikici bayan zaben shekarar 2007.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu