Kotun ICC ta bukaci a mika Ntaganda zuwa Hague
Kotun hukunta laifukan yaki ta ICC ta yi kira a hannunta Kwamandan ‘Yan tawayen Jamhuriyyar Congo Bosco Ntaganda zuwa Hague bayan ya mika kansa ga ofishin jekadancin Amurka a birnin Kigali.
Wallafawa ranar:
Ntaganda da ake kira da sunan "The Terminator", ana tuhumarsa ne da aikata laifukan yaki da cin zarafin bil’adama guda bakwai da suka hada da kisa da fyde da sa aikin bauta da kuma tursasawa yara shiga aikin Soji a kasar Jamhuriyar Congo.
A ranar Talata ne Ntaganda, mai shekaru 40 ya mika kansa ga ofishin jekadancin Amurka a Rwanda da ke makwabtaka da Jamhuriyyar congo.
Sai dai gwamnatin kasar Rwanda ta yi watsi da bukatar ICC, tana mai cewa wannan ya shafi Amurka da Gwamnatin Congo da kuma ICC.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu