Isa ga babban shafi
DRC Congo

Shugaban ‘Yan tawayen Congo, Ntanganda ya mika kansa ga hukuma

Shugaban ‘Yan tawayen kasar Jamhuriyar Demokradiyar Congo, Janar Bosco Ntaganda wanda kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ke nema ruwa jallo, ya mika kansa zuwa hukumomin ofishin jakadanci kasar Amurka dake Kigali a kasar Rwanda. Ministan harakokin wajen kasar ta Rwanda, Louise Mushikiwabo ne ya tabbatar da wannan lamari, inda ya bayyana cewa, gwamantin kasar na kokarin tattara bayanai akan abinda ya kai ga Ntaganda ya mika kansa.  

Shugaban 'Yan tawayen kasar Jamhuriyar Demokradiyar Congo, Bosco Ntaganda
Shugaban 'Yan tawayen kasar Jamhuriyar Demokradiyar Congo, Bosco Ntaganda Reuters
Talla

Kotun hukunta manyan laifuka na tuhumar Bosco Ntaganda da keta hakkin Bil adama da kuma irin rawa da ya taka a boren da wadansu ‘yan kasar suka yi, al’amarin da ya kai ga kafa kungiyar ‘yan tawayen kasar ta Jamhuriyar demokradiyar Congo da kuma tallafawa ‘yan kungiyar M23, inda har ila yau bayanai suka nuna cewa Ntaganda ya tilasawa yara kananan shiga aikin sojin.

A dai shekarar 2006 kotun ta ba da sammacin kamo Ntaganda da wadanda wasu ke wa lakabi da “Terminator,” wato mutumin dake gamawa da mutane.

Majalisar Dinkin Duniya ta nuna farin cikin ta jim kadan da samun labarin mika kansa da Ntaganda ya yi, sun kuma jaddada aniyarsu ta ganin an kawo karshen yakin dake addabar yankin kasashen Afrika ta tsakiya .

Kasar ta Rwanda na cikin kasashe goma da suka rattaba hanu a wata yarjejeniyar samar da zaman lafiya a kasar ta Jamhuriyar Demokradiyar Congo .
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.