Isa ga babban shafi
AU

Shugabanin Afrika sun amince da yarjejeniyar samar da zaman lafiya a kasar Congo

Shugabannin kasashen nahiyar Afrika sun cim ma yarjejeniyar  samar da zaman lafiya a kasar Jamhuriyyar Dimokradiyyar Congo  a babban taronsu a birnin Addis Ababa na kasar Habasha domin daukar matakin Soji don kakkabe 'Yan tawaye bayan kwashe shekaru kasar na cikin tashin hankali.

Taron majalisar kungiyar ECOWAS
Taron majalisar kungiyar ECOWAS
Talla

A cikin wannan yarjejeniyar haka ma shugabannin sun shirya karawa Dakarun kawance na Majalisar dunkin Duniya kwarin guiwa domin kakkabe ‘yan tawaye, bayan kwashe shekaru ana fama da Rikici a kasar ta Congo.

11 daga cikin kakashen dake kan iyaka da Teku, da kuma aka zarga da goyawa ‘yan tawaye masu tada Kayar-baya, na daga cikin wadanda suka rattaba Hannu ga yarjejeniyar a babban taron da aka gudanar a birnin Addis Ababa na kasar Ethiopia a gaban Sakataren Majalisar dunkin Duniya Ban Ki-Moon.

Sakataren majalisar dunkin Duniya Ban Ki-Moon, ya bayyana taron a matsayin somin tabi ga shirin dake bukatar dorewar zaman lafiya da fahimtar juna

Yayi fatar cewar kawancen kasashen na nahiyar Afruka zai taimaka ga samar da zaman lafiya da Lumana ga al’ummar kasar Congo.

An dai bayyana cewar shugabannin kasashen jamhuriyar Dimokradiyyar Congo, da Afruka ta kudu, da Mozambique, da Rwanda, da Tanzaniya duka sun halarci taron da aka rattaba Hannu kan wannan yarjejeniya

Baya ga wadannan ma akwai Jakadun kasashen Uganda da Angola da Burundi da Afruka ta tsakiya, da kuma Zambia.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.