Isa ga babban shafi
Mali

Dakarun Kasashen Yammacin Afrika sun karbe filin saukan jiragen Timbuktu

Rahotanni daga kasar Mali na na nuna cewa, dakarun kasashen Yammacin Afrika na ECOWAS ko kuma CEDEAO, wadanda ke samun jargorancin dakarun kasar Faransa, sun karbe ikon filin saukan jiragen garin Timbuktu.

Dakarun Najeriya rike da bindigoginsu suna sauka daga jirin sama
Dakarun Najeriya rike da bindigoginsu suna sauka daga jirin sama Bamada.net
Talla

A jiya rahotannin sun nuna cewa dakarun suna ta kutsa kai zuwa garin na garin Timbuktu, da ke arewacin kasar, yayin da suka kame garuwan da ke kan hanya.
 

Rahotannin da muke samu na cewa ba wata turjiyar da dakarun, masu aiki tare da na kasar Faransa ke samu, daga ‘yan tawayen masu kishin Islama.
 

Manjo Janar Shehu Usman Abdulkadin, Kwamandan rundunar sojojin na ECOWAS a kasar ta Mali, ya bayyana hakan a jiya, inda ya kara da cewa tuni an kwato garuruwa da dama wadanda a da ke hanun ‘Yan tawaye.

Sai dai ya kara da cewa, garin daya rage a kwato daga hanun ‘yan tawayen shine garin Timbuktu, wanda dakarun tuni sun karbe ikon filin saukan jiragen.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.