Isa ga babban shafi
Kenya-AU-ICC

Kasashen Afrika za su nemi kotun ICC ta janye tuhumar da ake wa Kenyatta

Ministocin kasahen Afrika sun amince da kudirin aikawa Kotun hukunta laifukan yaki ta ICC da bukatar dawo da shari’ar tuhumar da ake wa shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta da mataimakinsa William Ruto zuwa kotun Kenya.

Shugaban Keniya Uhuru Kenyatta da mataimakinsa William Ruto
Shugaban Keniya Uhuru Kenyatta da mataimakinsa William Ruto
Talla

Minsitan harakokin wajen kudancin Sudan Nhial Deng Nhial ya shaidawa kamfanin Dillacin labaran Faransa cewa zasu aikawa kotun ICC da bukatar a dawo da shari’ar a kasar Kenya, yana mai cewa kudirin ya samu karbuwa daga sauran Ministocin kasashen Afrika kafin gudanar da babban taron kasashen a Addis Ababa a ranar Lahadi.

A ranar 9 ga watan Juli ne shugaba Kenyatta da mataimakinsa Ruto za su gurfana gaban kotun Hague game da tuhumar keta hakkin mutane a rikicin da ya biyo bayan zaben shekarar 2007 inda aka samu hasarar rayuka sama da 1,000.

Tuni Kenyatta da mataimakinsa suka amince za su ba kotun ICC hadin kai.

Amma yawancin Shugabannin Afrika suna ganin kotun ICC ta fi mayar da hankali wajen farautar shugabannin Nahiyar ba tare da la’akari da laifukan sauran kasashen bangarorin duniya ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.