Lauyoyin Kenyatta sun bukaci a janye tuhumar da ake yi masa
Lauyoyin zababben shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta sun bukaci kotun hukunta laifukan yaki ta Duniya wato ICC da ta jingine tuhumar da take wa Uhuru Kenyatta, dangane da tashin hankalin siyasa da ya faru a shekarar 2007. Daya daga cikin Lauyoyin, Kenyatta, Steven Kay ya bukaci Alkalan Kotun su 3 da su cire Kenyatta daga karar da za’a shigar a watan Yuli.
Wallafawa ranar:
A cewarsa an gurgunta shaidun da aka gabatar kan zargin da aka yiwa Francis Muthaura wanda aka zarga tare da Kenyatta ne ta hanyar cire daya daga cikin shaidu masu muhimmanci.
Ya kara da cewa ya kamata a duba al’amari shi Uhuru Kenyatta ta hanyar sake duba zargin da ake masa da suka hada da fyade, da kisa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu