Isa ga babban shafi
Kenya

Kenyatta: Alkalan kotun duniya sun soki masu gabatar da kara saboda rashin gabatar da shaidu

Alkalan kotun duniya dake shari’ar manyan laifufuka, sun soki masu gabatar da kara kan yadda suka kasa gabatar da shaidun da za’a yiwa shugaban kasar Kenya, Uhuru Kenyatta shari’a.

Sabon shugaban kasar Kenya, Uhuru Kenyatta
Sabon shugaban kasar Kenya, Uhuru Kenyatta REUTERS/Noor Khamis
Talla

Ana zargin masu gabatar da kara ne da boye wani shaida, wanda keda matukar muhimanci a shari’ar, abinda ya sa aka sallami Francis Muthaura, mutumin da ake zargin sa tare da Uhuru Kenyatta.

Ana dai zargin sabon shugaban kasar ta Kenya ne da laifukan tunzura masu zanga zanga a fadan da ya barke a kasar a shekarar 2008 bayan an gudanar da zabe a karshen shekarar 2007 wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane sama da 3,000.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.