Isa ga babban shafi
Kenya

An rantsar da Uhuru Kenyatta a matsayin shugaban Kenya

Zababben shugaban kasar Kenya, Uhuru Kenyatta, ya karbi rantsuwar kama aiki a matsayin shugaban kasa na hudu, tun samun yancin kan kasar, sakamakon nasarar zaben da ya samu akan Raila Odinga.

Sabon Shugaban kasar Kenya Kenya Uhuru Kenyatta
Sabon Shugaban kasar Kenya Kenya Uhuru Kenyatta REUTERS/Presidential Press Service/Handout
Talla

Masana suna ganin duk da Uhuru Kenyatta yana fuskantar tuhumar aikata laifukan yaki daga kotun ICC amma suna ganin sabon shugaban zai ci gaba da alaka tare da amintaka da gwamnatocin kasashen Yammaci.

04:03

Bakonmu A yau:Hussaini Abdu na kungiyar Action Aid a game da zaben Kenya.

Abdoulkarim Ibrahim

A lokacin da ya ke yakin neman zabensa Uhuru Kenyatta ya yi amfani da kalaman nuna kiyayya ga kasashen Yammaci musamman huldar da ta shafi kasuwanci tsakanin Kenya da kasashen.

Sai dai masana suna ganin yana da wahala Kenyatta ya juyawa kasashen yammaci baya domin rungumar kasar China kamar yadda ya nuna a yakin neman zaben shi.

Shugaban Kenya na farko Jomo Kenyatta, shi ne Mahaifin Uhuru Kenyatta wanda ya jagoranci kasar bayan samun ‘Yancin kai a shekarar 1963.

Uhuru Kenyatta ya samu nasara ne akan abokin hamayyarsa Raila Odinga wanda a farko ya yi watsi da sakamakon zaben kafin daga bisani ya amince da sakamakon hukuncin kotun koli.

An samu nasarar kammala zaben Kenya ba tare da samun rikici ba.

Amma Kenyatta da mataimakinsa William Ruto suna fuskantar tuhuma a kotun hukunta laifukan yaki ta ICC da ke zargin sun taka rawa a rikicin zaben 2007 da ya yi sanadiyar mutuwar mutane sama da 1,000.

Kenyatta zai kasance shugaba na biyu da ke fuskantar tuhuma a kotun ICC bayan shugaban Sudan Omar Hassan al Bashir wanda ake tuhuma akan kisan kiyashin da aka aikata a yakin Darfur.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.