China ta yi kiran daukar matakin gaggawa a Najeriya bayan bindige ma’aikacinta
Gwamnatin kasar China ta yi Allah Waddai da kisan wani ma’aikacin kasar da aka bindige a Maiduguri tare da kiran mahukuntan Najeriya daukar matakin gaggawa domin kare rayukan ‘Yan kasashen Waje.
Wallafawa ranar:
A ranar Juma’a ne wasu ‘Yan bindiga suka bindige wani ma’aikacin Kamfanin kasar China a birnin Maiduguri wanda shi ne mutum na biyu dan kasar China da aka kashe.
Kakakin ma’aikatar harakokin wajen China Hong Lie ya ce sun dauki wannan al’amarin da muhimmci matuka. Tuni kuma ofishin jekadancin China ya mika takardar koke ga gwamnatin Najeriya da ke kira ga gwamnatin kasar daukar matakin gaggawa.
A ranar Bakwai ga watan Oktoba wasu ‘Yan bindiga sun kashe wani dan China a garin Gubio da ke kusa da Maiduguri.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu