Isa ga babban shafi
Pakistan-Lebanon Iran-Najeriya

An kai jerin hare hare a wasu sassan kasashen duniya

A yau juma’a akwai jerin hare hare da aka kai a wasu sassan kasashen duniya musamman a yankin Gabas ta tsakiya da kuma Najeriya. Hare haren sun yi sanadiyar mutuwar mutane da dama a kasashen Pakistan da Afghanistan da Iraki da Iran da kuma Najeriya.

Wani waje da aka kai hari a kasar Iraqi
Wani waje da aka kai hari a kasar Iraqi REUTERS/Stringer
Talla

Wani hari da aka dasa a keke ya yi sanadiyar mutuwar mutane uku tare da raunata wasu da dama a yankun kudu masu yammacin Pakistan.

A birnin Beirut kuma na kasar Lebanon wani hari da aka kai a yau Juma’a ya yi sanadiyar mutuwar mutane Takwas tare da raunata mutane sama da 70. Wannan harin kuma shi ne irinsa na farko tun bayan wani hari da aka kai a Beirut a shekarar 2008.
A kasar India kuma wasu ‘yan bindiga sun kai hari a ginin wata otel wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane biyu a yankin Kashmir.

Kazalika wani hari da ‘yan tawayen Kurdawa suka kai akan bututun man Iran ya raunata sojin Turkiya kusan 30.

A kasar Iraqi kuma wasu ‘Yan bindiga sun tayar da bom tare da bude wuta ga wata mota kirar bus da ke dauke da mahajjata. Harin dai ya yi sanadiyar mutuwar mutane Hudu tare da rauanta wusu matuenn 11.

Wani harin kuma da ake zargin ‘Yan kungiyar al Qaeda suka kai a kudancin Yemen ya yi sanadiyar mutuwar mutane 14.

A kasar Afghanistan kuma mutane 15 ne suka mutu a wani hari da aka kai ga wata mota kirar bus mai dauke da wasu baki da ke kan hanyarsu zuwa wajen buki. Yawancin wadanda suka mutu dai mata ne da yara kanana.

A Najeriya kuma rahotanni na cewa mutane da dama ne suka mutu a wasu jerin hare hare da aka kai a arewacin kasar.

Rahotannin na cewa tun a daren jiya ake jin karar fashewar bamai bamai da karar bindiga a garin potiskum.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.