Isa ga babban shafi
Najeriya

An ji karar bindiga da harin Bom a Potiskum

An ji karar fashewar Bom da harbin bindiga a garin Potiskuma a Arewa maso gabacin Najeriya a jiya Laraba, bayan wani rikicin da ya lakume rayukan mutane 24 a garin Maiduguri. Mazauna garin sun ce suna zaman dar dar, amma ba su da tabbacin ko Jami’an tsaro ne ke musayar wuta da ‘Yan bindiga.

Masallcin Juma'a a Maiduguri
Masallcin Juma'a a Maiduguri REUTERS/Olatunji Omirin
Talla

Wani mazauni Potiskum ya shaidawa kamfanin dillacin labaran Faransa cewa sun ji karar fashewa da misalin karfe 5:50 na safe daga bisani kuma suka ji karar harbe harbe.

Rahotanni sun ce ana harbe harben ne a unguwar da Bakuna suke da barikicn Soji a Potiskum.

A jiya Talata ne Jami’an tsaro suka ce sun kashe ‘Yan kungiyar Boko Haram 24 a garin Maiduguri bayan wani hari da ake zargin ‘Yan kungiyar sun kaddamar.

Ana zargin Jami’an tsaro da wuce gona da iri wajen kashe fararen hula da suna farautar ‘Yan kungiyar Boko Haram.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.