Najeriya: An kafa dokar hana fita a garin Mubi
Gwamnatin Jihar Adamawa dake Nigeria, ta kafa dokar hana fita a garin Mubi, saboda kisan da aka yiwa mutane 26 a garin, akasarin su daliban babbar Kwalejin Fasaha ta Gwamnatin Tarayya. Tuni dai aka rufe makarantar, kuma rahotanni sun ce kisan ya jefa fargaba ga daukacin mutanen garin. Rundunar ‘Yan Sanda da sauran jami'an tsaro a jihar Adamawa dake Nigeria sun kaddamar da farautar wasu mutane da suka kashe dalibai 26 yau da safe a garin Mubi.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Daliban na karatu ne a Makarantar koyon Sana'oi da ake kira Federal Polytechnic Mubi.
Bayanai na nuna maharan sun bi gida-gida ne da daliban ke zama, suna kiran sunayen daliban daya- bayan-daya suna kashewa.
Kakakin Rundunar 'Yan sandan jihar Adamawa, DSP Mohammed Ibrahim ya gaskata aukuwan wannan al'amari, bayan ya ziyarci inda lamarin ya auku tare da sauran jamian tsaro dake jihar.
Maimagana da yawun Hukumar bada agajin gaggawa ta Tarayya y ace rahotanni sun nuna cewa, daliban da aka kashe ‘Yan takara ne a wani zabe da aka gudanar a kwalejin.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu