Isa ga babban shafi
Najeriya

HRW ta zargi Jami’an tsaron Najeriya da keta hakkin Bil’adama

Hukumar kare hakkin bil’adama ta Human Rights Watch ta yi zargin Jami’an tsaron Najeriya da Kungiyar Boko Haram da laifin keta hakkin Bil’adama a rikicin kasar da ya yi sanadiyar mutuwar mutane kimanin 3,000.

Jami'an tsaron Najeriya suna sintiri a saman titi bayan saka dokar hana Fita a cikin biranen Arewacin kasar
Jami'an tsaron Najeriya suna sintiri a saman titi bayan saka dokar hana Fita a cikin biranen Arewacin kasar sphotos-a.xx.fbcdn.net
Talla

Rahoton Hukumar da aka fitar mai yawan shafi 98 ya zayyana laifukan keta hakkin bil’adama da Jami’an tsaro da kungiyar Boko Haram suka aiwatar wadanda suka kunshi kisa da gallazawa tare da satar kayayyakin mutane bayan kai hare hare.

An kwashe tsawon lokaci ana fama da hare haren bama bamai a arewacin Najeriya da ake zargin Kungiyar Boko Haram da aikatawa tare da zargin Jami’an tsaro wajen gallazawa tare da kisan mutanen da ba su ji ba su gani ba.

A makon jiya an samu mutuwar mutane 30 a wani samame da Sojoji suka kai a birnin Maiduguri tushen ‘Yan kungiyar Boko Haram. Amma rundunar Sojin kasar ta musanta zargin.

Rahoton Hukumar Human rights Watch ya yi kiran gudanar da bincike tare da neman hukunta Sojoji da ‘Yan Sandan da suka aikata laifin keta hakkin Bil’adama.

Hukumar kuma ta kalubalanci gwamnatin Najeriya game da yin sakaci wajen kula da sha’anin ‘Yan kungiyar Boko Haram.

Kungiyar Boko Haram dai ta kaddamar da hare hare ne a Najeriya tun bayan kashe shugabanta Muhammed Yusuf da Jami’an tsaro suka yi a zamanin mulkin Marigayi Ummaru Musa ‘Yar’Adua.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.