Isa ga babban shafi
US

Shugaban Amurka Obama ya katse ziyara Turai don komawa gida saboda tarzoma a Dallas

Shugaban  Amurka Barack Obama na shirin katse halartan taro da ya ke halarta a Turai don komawa kasar sa ya tafi ganin irin abinda ya faru a Dallas inda aka yi wa wasu ‘yan sanda kwanton bauna aka kashe biyar bayan da aka sami kisan bakaken fata farar hula biyu da ake zargi aikin 'yan Sanda fararen fata ne da ba sa son bakaken fata.

An sassauto kasa da tutoci a Amurka saboda rikicin Dallas
An sassauto kasa da tutoci a Amurka saboda rikicin Dallas REUTERS/Mike Segar
Talla

Fadar shugaban kasar sun bayyana cewa Barack Obama ya amsa goron gayyata ne daga Magajin garin Dallas,  Mike Rawlings ya je makon gobe domin ganewa idanun sa abubuwan da suka faru.

Bayanai na nuna dan bindigan daya kashe ‘yan sandan mai suna Micah Johnson dan shekaru 25  tsohon soja ne wanda bashi da wani tarihin aikata laifuka.

David Brown Jami'in ‘yan sanda a Dallas ya fadi cewa ‘yan sanda sun gano tarkacen hada bam da wasu makamai a gidansa, bayan da ya aikata kisan ‘yan sandan, amma kuma an gano cewa gaban kansa yayi, babu hannun wata kungiya a ciki.
 

Tuni dai Shugaba Obama ya umarci a sassauto da tutocin kasar kasa alamun juyayi na abin da ya faru.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.