Isa ga babban shafi

'Yan tawayen Houthin Yemen sun ce sun kai hari kan jiragen ruwa 98

'Yan tawayen Houthi na kasar Yemen da ke samun goyon bayan Iran sun ce sun kai farmaki kan jiragen ruwa kusan 100 a tekun Bahar Maliya da Tekun Aden a cikin watannin da suka shafe suna kai hare-hare abin da ya kawo cikas ga zirga-zirgar jiragen ruwa a duniya.

Wani jirgin ruwan Indiya da  ya hadu da ibtila’in harin mayakan Houthi a tekun Aden, ranar 18 ga watan Janairu, 2024.
Wani jirgin ruwan Indiya da ya hadu da ibtila’in harin mayakan Houthi a tekun Aden, ranar 18 ga watan Janairu, 2024. © Marine indienne via AP
Talla

A wani jawabi da tashar Al-Masira ta 'yan tawayen ta yada, ta nuna yadda shugaban Houthi Abdel Malek al-Huthi ke sanar da sabbin hare-hare kan jiragen ruwa 8, tare da cewa a halin yanzu jimillar jiragen ruwa masu alaka da abokan gaba guda 98 suka kaiwa hari.

Hare-haren da aka kai kan jiragen ruwa da ake ganin suna da alaka da Isra'ila ko kawayenta sun yi matukar tasiri.

A watan Nuwamba ne mayakan na Houthi suka fara kai hare-hare kan jiragen ruwa a mashigin tekun Aden da kuma tekun Red Sea, wani shiri da suka ce an yi shi ne a matsayin nuna goyon baya ga Falasdinawa a yankin Zirin Gaza da fuskantar hare-haren Isra’ila.

Hare-haren na Houthi, wanda ya kawo cikas ga zirga-zirgar jiragen ruwa, musamman masu dakon kayayyaki, na fuskantar ramuwar gayya daga dakarun Amurka da na Birtaniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.