Isa ga babban shafi
Amurka

An samu guba a wasikar da aka aikawa Barack Obama

An samu burbushin guba a wasu wasiku da aikewa Shugaban kasar Amurka Barack Obama da wani dan majalisar dattawan kasar, a yayin da aka umurci mutane su kauracewa wasu ofisoshin wasu ‘Yan majalisu guda biyu bayan an samu wasu wasiku makamantan haka. Hukumar bincike ta FBI ta bayyana cewa wasikar da aikawa Obama, wacce aka dakile isarta zuwa shugaban na dauke ne da burbushin gubar da ake kira Ricin wacce ba a samun maganinta.  

Shugaban kasar Amurka, Barack Obama
Shugaban kasar Amurka, Barack Obama REUTERS/Kevin Lamarque
Talla

Rahotanni na nuna cewa jami’an tsaron na boye ne suka samu wasikar a wani wuri da ake tantance wasikun da za a shiga da su cikin Fadar shugaban kasar ta White House.

Har ila yau an samu irin wasikar dauke da sunan dan majalisa Roger Wicker dauke da burbushin gubar.

Jami’an hukumar ta FBI sun ce wasikun guda biyu na da alaka domin akwai alamun garin daga Memphis a Jihar Tennessee aka aiko da su, an kuma saka kwanan watan 8 ga Aprilu.

A cewar rahotanni, a jikin wasikun an samu alamar saka hanu da aka rubuta kamar haka; “Nine KC, nine kuma na ba da umurnin wannan sako.”

Gano wadannan wasiku ya biyo bayan harin bama bamai da aka kai a birnin Boston wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane uku ciki har da yaro dan shekaru takwas.

Izuwa lokacin hada wannan rahoto babu wata sanarwa da ta fito daga Fadar ta White House game da wannan lamari.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.