Isa ga babban shafi
Amurka-Marathon

An gano abubuwan da aka yi amfani da su wajen kai harin Marathon a Boston

An shiga kwanaki uku a ci gaba da binciken gano wadanda ke da alhakin kai harin tseren gudun gasar Marathon a Boston kasar Amurka da ya kashe mutane uku tare da raunanata sama da 170. Hukumar bincike ta FBI ta nuna wasu hotunan da ke da alaka da kai harin.

Wani Abu da aka gano an yi amfani wajen kai harin Marathon a Boston kasar Amurka
Wani Abu da aka gano an yi amfani wajen kai harin Marathon a Boston kasar Amurka REUTERS
Talla

Har yanzu dai ana ci gaba da gudanar da bincike amma an gano wasu abubuwa da aka yi amfani da su wajen haka bom da ya tashi a Boston.

Ana sa ran Shugaban Amurka Barack Obama zai kai ziyara Boston a ranar alhamis wanda ya bayyana harin a matsayin harin ta’addanci.

Akalla mutane uku aka ruwaito sun mutu kuma wasu mutane sama da 100 suka jikkata sakamakon fashewar bama bamai guda biyu.

Har yanzu ana lalaben wadanda suka dasa bama baman da suka tashi guda biyu. Kodayake an ji karar na uku amma jami’an tsaro sun ce yana da nasaba da wuta.

Jami’an tsaron Amurka sun ce sun yi nasarar warware wasu bama baman guda biyu da aka dasa.

Lamarin ya faru ne a lokacin da ‘Yan tseren gudun na Marathon suna zangon karshe.

Wannan ne karo na 117 da ake gudanar da gasar tseren gudun na Marathon a Boston, wanda shi ne wasa na biyu da ke jan hankalin Amurkawa bayan wasan Super Bowl.

‘Yan tseren gudu kimanin 28,000 ne suka shiga gasar daga yankunan Amurka da kuma wakilai daga kasashe sama da 90.

‘Yan tseren gudun Kenya ne a kan gaba.

Kuma ana gudanar da tseren gudun ne a dai dai lokacin da gwamnatin Jahar Massachusetts ta ware hutu domin tunawa da karrama juyin juya halin Amurka a wajajen 1775.

Wannan dai shi ne hari mafi muni da aka kai tun bayan harin 11 ga watan Satumba. Shugaban Amurka Barack Obama yace za su yi farautar wadanda suka kai hare haren a cikin ‘yan kallo da suka tsaya saman tituna suna kallon tseren gudun.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.