Isa ga babban shafi
Amurka

Shugaban kasar Amurka Barack Obama ya zabi Jack Lew ya maye gurbin sakataren Baitil-Mali Timothy Geithner

Shugaba Barack Obama, zai mika sunan Jack Lew, ga ‘Yan majalisar Dattawan kasar, a matsayin wanda zai maye gurbin, Sakataren Baitil-Mali, Timothy Geithner.Dan shekaru 57, Jack Lew ya kasance shine Babban Hafsa a fadar White House, wanda a da ya taba rike mukamin Shugaba Mai kula da Ofishin Kasafin kudin kasar ta Amurka.  

Shugaban kasar Amurka Barack Obama, yake jawabi
Shugaban kasar Amurka Barack Obama, yake jawabi REUTERS/Kevin Lamarque
Talla

Kafofin yada labaran kasar ta Amurka ne, a yau suka bayyana yiyuwar zaben Lew a matsayin sabon Sakataren Baitulmalin kasar, sai dai izuwa lokacin hada wannan rahoto, Fadar ta White House bata tabbatar, kota musanta labarin ba, duk da cewa wata majiya ta ce ba a dauki kwakwarar matsaya akan zaben na Lew ba.

Shi dai tsohon Sakataren Baitulmalin kasar, Timothy Geithener, kamar yadda rahotanni ke nunawa, ya bayyana cewa ba shi da sha’awar ya sake kasancewa a wannan mukamin nashi a wannan wa’adin gwamnatin na biyu.

Mutane da yawa kuma na ganin Geithner, wanda zai ajiye aikinsa a karshen watannan, ya kasance muhimmi wajen kokarin da gwamnatin ta Obama ke yi na ganin an sake raya tattalin arzikin kasar tun bayan tabarbarewar al'amurra, inda wasu da dama ke ikrarin cewa ya taka rawar gani wajen kaucewa matsalar sake durkushewar tattalin arzikin kasar da aka yi nasara a satin da ya gabata, inda aka yi ta takaddama akan kasafin kudin kasar na bana.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.