Isa ga babban shafi
Amurka

Obama ya yi sabbin nade nade

Shugaban kasar Amirka Barack Obama ya yi sabbin nade-nade, da suka hada da na Sakataren tsaro da kumasabon Daraktan Hukumar Leken Asiri ta CIA. Obama, ya gabatar da sunan tsohon Dan Majalisar Dattijai Chuck Hagel a matsayin sakataren tsaron, inda ya yi ta yabon sa a matsayin mutun da ba ya da kwalo-kwalo.

Shugaban Amurka Barack Obama tare da  Chuck Hegel sakataren da John Brennan Shugaban  CIA
Shugaban Amurka Barack Obama tare da Chuck Hegel sakataren da John Brennan Shugaban CIA AFP PHOTO/Brendan SMIALOWSKI
Talla

Shugaba Obama yace Chuck Hagel mutum ne mai kishin Amurka ne, ganin yadda ‘yan majalisa daga bangaren Republican suka rika kushe shi saboda kalamansa game da kasar Isra’ila.

A cewar Shugaba Obama Chuck Hagel wanda ya samu sabani da jam’iyyarsa ta Repulican saboda ya kushe yakin da kasar Amurka ta kulla da kasar Iraki, ya cancanci a jinjina masa saboda tsananin kishin kasa da ya ke da shi.

Shugaba Obama ya kuma gabatar da sunan John Brennan a matsayin wanda zai bai wa mukamin Babban Daraktan Hukumar Leken CIA, wanda zai maye gulbin David Petraus.

A cewar Shugaba Obama, John Brennan, gwani ne.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.