Isa ga babban shafi
Syria-Amurka

Obama ya amince da Gwamnatin ‘Yan tawayen Syria

Shugaban Kasar Amurka, Barack Obama, ya bayana amincewar shi da shugabanin ‘Yan Tawayen Syria, a matsayin halattattun wakilan al’ummar kasar. Obama yace, sauyin da aka samu a hadaddiyar kungiyar, wadda ta kunshi bangarori dabam dabam, ya nuna cewar, an samu hadin kai a tsakanin bangarorin ‘Yan Tawayen.

Shugaban Amurka  Barack Obama
Shugaban Amurka Barack Obama REUTERS/Larry Downing
Talla

A kokarin da Amurka na kokarin ganin ‘Yan tawayen sun cim ma nasarar hambarar da Gwamnatin Bashar Al Assad, Gwamnatin Obama ta saka sunan kungiyar Al Nusra cikin jerin sunayen kungiyoyin ‘Yan ta’adda saboda alakarta da kungiyar Al Qaeda.

Ana dai zargin kungiyar Al Nusra da kokarin karkatar da juyin juya halin da kasashen Syria ke yi.

Tuni dai kasashen Faransa da Birtaniya da turkiya da wasu kasashen Turai suka amince da Sabuwar Gwamnatin ‘Yan tawayen na Syria.

Gwamnatin kasar Rasha aminiyar Syria tace ta yi mamakin yadda Amurka ta amincewa da ‘Yan tawayen.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.