Isa ga babban shafi
Amurka

Susan Rice ta jingine takarar kujerar Sakatariyar Harakokin wajen Amurka

Susan Rice Jekadariyar Amurka a Zauren Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci Shugaba Barack Obama kada ya nada ta Sakatariyar harakokin wajen kasar a Gwamnatin shi a matsayin wadda za ta gaji Hillary Clinton.

Jekadiyar Amurka a zauren Majalisar Dinkin Duniya Susan Rice
Jekadiyar Amurka a zauren Majalisar Dinkin Duniya Susan Rice Reuters
Talla

Susan Rice ta taka muhimmiyar rawa wajen kawo karshen sukar da Jam’iyyar Republican ke yi wa Gwamnatin Obama game da rikicin Benghazi da aka kashe Jekadan Amurka a ranar 11 ga watan Satumba.

Rice ta aikawa Shugaba Obama da Wasika tana mai cewa aikin yana da matukar wahala da dauke hankali wanda ya shafi kare muradun Amurka a Duniya.

Matakin ba Rice mukamin sakatariyar harakokin wajen Amurka na zuwa ne saboda hasashen Obama yana gab da bayyana sunan jami’an tsaro a gwamnatin shi. Kuma bayanai daga fadar White House na cewa Senata Chuck Hagel Obama zai nada Sakataren tsaron Amurka.

Masu Adawa da Susan Rice

‘Yan Jam'iyyar Republican dai sun soki Susan Rice bayan ta marawa Obama baya game da rikcin Benghazi inda tace al’amarin  ya faru ne sakamakon bacin ran Musulmi a Libya saboda fito da hoton da ya ci Zarafin addininsu.

Wasu ‘Yan adawa dai suna zargin Susan Rice akan rawar da ta taka a diflomasiyar Amurka a Nahiyar Afrika a zamanin mulkin Bill Clinton.

Rahotanni daga Amurka na nuni da cewa Senator John Kerry shi ne zai karbi mukamin idan har Obama bai zabi Susan Rice ba.

Senato John McCain Wanda ya kara da Obama a zaben Shugaban Amurka a shekarar 2008 yana cikin manyan masu adawa da matakin ba Susan Rice mukamin Sakatariyar Harakokin Wajen Amurka.

Mista McCain yace zai ci gaba da bincike har sai ya gano gaskiyar abinda ya faru a Benghazi inda rayukan Amurka Hudu suka salwanta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.