Isa ga babban shafi
Amurka

Kotun Amurka ta yanke hukuncin dauri ga mawallafin Bidiyon da ya ci mutuncin Musulunci

Kotun Amurka ta yanke hukuncin shekara guda ga Mark Basseley Youssef wanda ya fito da Faifan Bidiyon da ya haifar da zanga-zanga a kasashen Musulmi saboda cin zarafin Manzon Allah.

Nakoula Basseley Nakoula lokacin da 'Yan Sanda ke masa Rakiya daga gidansa a Los Angeles
Nakoula Basseley Nakoula lokacin da 'Yan Sanda ke masa Rakiya daga gidansa a Los Angeles Reuters/
Talla

Mark Basseley Youssef mai shekaru 55 zai kwashe shekara guda a gidan yarin Amurka bayan amsa laifin ya yi amfani da hutunan karya game da shi a lokacin da yake mu’amula da banki a shekarar 2010.

Kotun ta daura masa laifin tayar da hankalin Musulmi da ba su ji basu gani ba saboda Bidiyon da ya fitar wanda ya yi sanadiyar kai wa Ofishin jekadancin Amurka hari a kasar Libya.

Tun a shekarar 2009 ne ake tuhumar Mista Youssef wajen satar kudaden masu ajiya a banki kudi Dala 860. A watan Satumba ne aka Cafke kafin yanke masa hukunci a jiya Laraba bayan amsa laifuka Hudu na cin amanar Banki.

Mista Youssef ya sha yin amfani da sunaye da dama musamman ya yi amfani da sunan Nakoula Basseley Nakoula, da Sam Bacile lokacin da ya yada Bidiyon cin zarafin Manzon Allah.

A ranar 11 ga watan Satumba ne Musulman kasar Libya suka kai wa Ofishin jekadancin Amurka hari a Benghazi inda suka kashe jekadan Amurka Chris Stevens da waus Jami’an Diflomasyar kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.