Isa ga babban shafi
Amurka-Libya

Clinton ta dauki alhakin matsalar da aka samu a Benghazi

Sakatariyar Harkokin wajen murka, Hillary Clinton, ta dauki alhakin matsalar tsaron da aka samu a Benghazi, abinda ya yi sanadiyar kashe Jami’an Diflomasiyar Amurka a wani bore da Musulmin Libya suka gudanar bayan fitar da hoton Bidiyo da ke cin zarafin Manzon Allah.

sakatariyar harakokin wajen kasar Amruka, Uwargida Hillary Clinton a lokacin da ta ke amsa daukar alhakin matsalar da aka samu a Benghazi
sakatariyar harakokin wajen kasar Amruka, Uwargida Hillary Clinton a lokacin da ta ke amsa daukar alhakin matsalar da aka samu a Benghazi REUTERS/Jorge Luis Baca
Talla

Clinton tace ta dauki matakin ne don kawo karshen cece kucen da ya mamaye kasar ta Amurka, musaman a wannan lokacin da ake fuskantar zabe.

‘Yan Jam’iyar Republican sun zargi shugaba Barack Obama da rashin daukar matakan da suka dace wajen kare jami’an, da kuma rashin hukunta wadanda suka yi sakaci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.