Isa ga babban shafi

An kashe wani jami’in Diflomasiyar Amurka a Libya

Masu zanga-zanga a kasar Libya da Masar sun kai hari ofishin jekadancin Amurka da ya yi sanadiyar mutuwar wani babban Jami’in Diflomasiyar Amurka a Benghazi a wata zanga-zangar nuna bacin rai ga wani Fim da wani Dan kasar Masar, mazaunin Amurka ya yi, da ke nuna cin zarafin Manzon Allah.

Masu Zanga-zanga a birnin Benghazi na kasar Libya
Masu Zanga-zanga a birnin Benghazi na kasar Libya
Talla

Sakatariyar harakokin wajen Amurka Hillary Clinton, ta tabbatar da mutuwar Jami’in da aka kashe a Banghazi tare da yin Allah Waddai da harin.

A kasar Masar, masu zanga zangar, sun kai hari a ofishin Jakadancin Amurka, inda suka yaga tutar kasar, tare da maye gurbin tutar da wata tutar Islama.

Kakakin gwamnatin kasar Libya Abdel-Monem Al-Hurr, yace akwai alaka tsakanin zanga zangar Benghazi da kuma zanga-zangar da aka gudanar a birnin al Kahira.

A jiya Talata lokacin da Amurka ke bukin tuna harin 11 ga watan Satumba Wani Fasto mai suna Terry Jones yace ya fitar da wani faifan Bidiyo da ke nuna hoton Manzon Allah.

Wannan Bidiyon ne kuma ya haifar da zanga-zanga a kasar Masar, inda daruruwan Musulmi suka yi gangami a birnin al Kahira domin nuna fushin cin zarafin Musulunci,Tare da kira ga shugaban kasar Masar Muhammed Mursi ya dauki mataki akai.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.