Isa ga babban shafi
Pakistan-Amurka

Bayanin kisan Osama daga bakin likitan da ya taimaka aka kashe shi

Wani Likitan Pakistan, Shakil Afridi wanda ya taimaka aka gano mabuyar Shugaban al Qaeda Osama bin Laden yace baya da masaniyar da sa hannun shi wajen kisan Osama a bara a lokacin da ya ke zantawa da kafar yada labaran Fox.

Shakeel Afridi. Likitan da ake zargin ya taimaka aka kashe Osama
Shakeel Afridi. Likitan da ake zargin ya taimaka aka kashe Osama REUTERS/Geo News via Reuters TV
Talla

Dakta Afridi wanda ke Magana a karon farko, yace bai yi tunanin tserewa ba bayan samun labarin kisan Osama amma Jami’an leken asirin Pakistan ne suka yi garkuwa da shi.

A cewar Dakta Afridi wadanda suka yi garkuwa da shi sun gallaza ma shi azaba sannan sun dauki Amurka a matsayin babbar Makiyarsu.

Babu dai wani bayani akan yadda aka tattauna da Dakta Afridi wanda ke kulle a gidan Yarin Peshawar.

Ana zargin Afridi ne da yin amfani da rigakafin maganin hepatitis B domin daukar samfarin jinin iyalan Osama.

A watan Mayu ne aka yanke wa Dakta Afridi hukuncin daurin shekaru 33 akan zargin taimakawa da tallafawa ta’addanci.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.