Isa ga babban shafi
Pakistan

Wata Kotun Pakistan ta yanke hukunci dauri ga Iyalan Osama

Wata kotun Kasar Pakistan ta yanke wa Iyalan Osama bin Laden hukuncin dauri kwanaki 45 a gidan yari tare da ‘Yayansa mata biyu, bayan kama su da laifin shiga kasar ba tare da izini ba tare da bada umurnin fitar da su daga Pakistan.

'Yan Sandan Pakistan a harabar gidan da aka Cafke matan Osama  a Islamabad
'Yan Sandan Pakistan a harabar gidan da aka Cafke matan Osama a Islamabad REUTERS/Faisal Mahmood
Talla

Matan Osama biyu ne ‘Yar kasar Saudiya da Yemen Kotun ta yankewa hukuncin wadanda ke zaune a Pakistan tun lokacin da dakarun Amurka suka kashe Mijinsu Osama a birnin Abbottabad ranar Biyu ga watan Mayu a shekarar 2011.

A jiya Litinin ne Kotu ta yanke hukuncin bayan kwashe sa’oi uku ana zaman kotun.

Lauyan da ke kare matan Muhammad Aamir, yace hukuncin daurin kwanaki 45 zai fara aiki a ranar uku ga watan Maris da aka cafke matan, sai dai yace za’a kwashe mako biyu kafin a fice dasu daga Pakistan.

Dan uwan Matar Osama ‘Yar kasar Yemen, Zakarya Ahmad Abd al-Fattah, ya shaidawa manema Labarai akwai kudaden tara da aka bukaci matan su biya Dala $110, kuma yace Matan sun biya kudaden.

An bayyana wasu matan Osama guda biyu da Sunan Khairat Sabar da Siham Sabar bayan, matarsa ‘Yar kasar Yemen Amal Abdulfattah, kuma karkashin dokar kasar Pakistan za’a iya daure matan tsawon shekaru Biyar.

A wani Rehoto da ‘Yan Sandan Pakistan suka fitar sun ce Osama ya kwashe tsawon shekaru 10 yana buya a Pakistan bayan kai harin 11 ga watan Satumba da Amurka ke zargin shi da Jagoranta.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.