Isa ga babban shafi
Pakistan

Pakistan ta kori iyalan Osama zuwa Saudiya

Gwamnatin Pakistan ta kori iyalan marigayi Osama bin Laden zuwa Saudiyya da suka kunshi ‘Yayansa da matansa uku. Iyalan Osama sun kwashe lokaci suna zaune a Pakistan tun bayan da dakarun Amurka suka kashe shi a watan Mayun bara.

Matan Osama da 'Yayansa cikin wata motar Bus da aka samu hotun an dauko su daga Islamabad zuwa Filin zirgin sama da zai dauke su zuwa Saudiyya
Matan Osama da 'Yayansa cikin wata motar Bus da aka samu hotun an dauko su daga Islamabad zuwa Filin zirgin sama da zai dauke su zuwa Saudiyya REUTERS/Faisal Mahmood
Talla

Matakin korar iyalan na zuwa ne mako a cika shekara da kisan Osama.

Pakistan ta sallami iyalan Osama ne domin daidaita danganta da kasashen Turai da Amurka wadanda suka yi zargin tana goyon bayan ‘Yan kungiyar Al Qaeda.

A ranar 2 ga watan Mayu ne dakarun Amurka suka kashe Osama a gidansa da yake buya a Abbottabad gabas da birnin Islamabad ba tare da sanin Gwamnatin Pakistan ba, amma Bayan kashe shi ne gwamnatin Pakistan ta cafke ‘yayansa da matansa.

Matan Osama guda biyu ‘Yan asalin kasar Saudi Arebiya ne amma daya daga cikinsu ‘Yar kasar Yemen ce.

‘Yayan Osama mata Biyu sun kwashe kwanaki 45 a tsare a wani gida a Islamabad.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.