Isa ga babban shafi
Libya

Ministan cikin gidan Libya ya yi murabus

Ministan cikin gidan kasar Libya, Fawzi Abdelali ya yi murabus, saboda tabarbarewar tsaro a kasar bayan samun hare haren bama bamai da rikicin kabilanci da janyo r ruguza wani wajajen ibada a birnin Tripoli.

Ministan cikin gidan kasar Libya  Fawzi Abdel A'al  wanda ya yi murabus bayan kalubalantar shi game da sha'anin tsaro
Ministan cikin gidan kasar Libya Fawzi Abdel A'al wanda ya yi murabus bayan kalubalantar shi game da sha'anin tsaro REUTERS/Ismail Zitouny/Files
Talla

Wani jami’I a ofishin ministan, ya shaida wa kamfanin Dillacin labarun Faransa na AFP, cewa ministan ya ajiye mukamin shi, don nuna adawa da ‘Yan majalisar kasar wadanda suka dora laifin ga gwamnati.

Al’ummar kasar Libya sun yi ta Allah waddai da matakan da jami’an tsaron kasar suka dauka, bayan da wasu bama bamai suka tashi a lokacin bukin Sallar Eid El fitr, da kuma harin da aka kai a wasu wuraren ibada.

Daruruwan mutane ne suka fito a birnin Tripoli a ranar Lahadi domin zangar zangar neman inganta sha’anin tsaro tare da adawa da ruguza wajajen ibada.

Tun faduwar gwamnatin Gaddafi ‘Yan tawayen Libya suka karbe ragamar tafiyar da sha’anin tsaro a kasar karkashin ma’aikatar ayyukan cikin gida.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.