Isa ga babban shafi
Libya-Tunisia

Tunisia ta mika Baghdadi ga mahukuntan Libya

Hukumomin Kasar Tunisia, sun mika Tsohon Firaministan Libya, al Baghdadi al Mahmoudi ga mahukuntan kasar Libya, bayan ba shi mafaka a kasar a lokacin da ‘Yan tawaye suka karbe ikon birnin Tripoli a watan Satumba da har ya yi sanadiyar kawo karshen mulkin gwamnatin Marigayi Kanal Gaddafi.

Al-Baghadi al-Mahmoudi a lokacin da ya ke isa birnin Tripoli
Al-Baghadi al-Mahmoudi a lokacin da ya ke isa birnin Tripoli REUTERS/Anis Mili
Talla

Sai dai akwai sabani da aka samu tsakanin Shugaban kasar Tunisia da Firaminista wadanda ke da sabanin ra’ayin game da mika al Baghdadi ga mahukuntan Libya.

Sanarwar Mika Baghdadi ta fito ne daga Ofishin Firaministan kasar Hamadi Jebali.

Shugaban kasar Tunisia Moncef Marzouki wanda ke ziyara a kudancin Tunisia a wani bukin shekaru 70 na kafa rundunar Sojin kasar ya bayyana adawar shi game da mika Tsohon Firaministan yana mai cewa matakin ya saba doka.

Kungiyoyin fararen hula da lauyoyin kare hakkin Dan Adam, sun bayyana rashin amincewarsu da mika Baghdadi zuwa Libya, saboda rashin adalcin da zai fuskanta a wajen shari’a.

A ranar 21 ga watan Satumba ne aka Cafke Baghdadi a Tunsia a lokacin da ya ke kokarin tserewa zuwa Algeria.

Baghdadi shi ne Firaministan Gwamnatin Gaddafi tun a shekarar 2006 har zuwa faduwar gwamnatinsu a bara.

Yanzu haka dai Firaministan Libya Abdel Rahim al-Kib ya yi alkawalin kare ‘Yancin tsohon Firaministan a Libya.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.