Isa ga babban shafi
Libya

An dage zaben Libya zuwa ranar 7 ga watan Yuli

Hukumar Zabe a kasar Libya, ta dage zaben ‘Yan Majalisun da zasu rubuta kundin tsarin mulki, zuwa ranar 7 ga watan Yuli, Zabe na farko da za’a gudanar kawo karshen mulkin shekaru 40 na Kanal Gaddafi.

Alkalin Alakalai kotun kolin Libya, Kamal Bashir Dahan a lokacin da yake ganawa da Mambobin kwamitin kundin tsarin mulkin kasar
Alkalin Alakalai kotun kolin Libya, Kamal Bashir Dahan a lokacin da yake ganawa da Mambobin kwamitin kundin tsarin mulkin kasar REUTERS/Ismail Zitouny
Talla

A ranar 19 ga watan Yuni aka shirya gudanr da zaben, amma shugaban hukumar, Nuri al Abbar, yace yanzu sai watan gobe ne za’a gudanar da zaben saboda tsaikun da aka samu wajen amincewa da dokar shirya zaben.

‘Yan kasar Libya Kimanin Miliyan 2.7 ake sa ran zasu kada kuri’a a zaben kusan kashi 80 na al’ummar kasar.

Tuni dai kungiyar Tarayyar Turai ta aika da wakilanta da zasu sa Ido a zaben.
A ranar 20 ga watan Octoba ne ‘Yan tawayen Libya suka kashe Kanal Gaddafi bayan kwashe watanni ana gwabza yakin adawa da gwamnatin shi.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.