Isa ga babban shafi
Amurka

Yau Obama zai rantsar da sabun Sakataren kasar Amurka

Yau ake saran shugaban kasar Amurka, Barack Obama, zai nada Tsohon Dan Majalisar Dattawa daga Jam’iyar Republican, Chuck Hagel, a matsayin Sakataren Tsaron kasar, dan maye gurbin Leon Panetta. Bayanai na nuna cewar, Yan Jam’iyar republican na adawa da nadin, saboda abinda suka kira matsayin Hagel na adawa da kasar Isra’ila.  

Shugaban kasar Amurka, Barack Obama.
Shugaban kasar Amurka, Barack Obama. REUTERS/Jonathan Ernst
Talla

Senata Lindsay Graham daga Jihar South Carolina, ya bayyana damuwar sada shirin nada Hagel, inmda ya bayyana cewa idan an amince da nadin Hagel a matsayin Sakataren harkokin wajen Amurka, zai zama Sakatare na farko dake kiyayay da israila a tarihin Amurka,

Ya kara da cewa, Hagel na daga cikin wadanda suka bukaci tattaunawa da Iran, da kuma bukatar Isra’ila ta tattaunawa da kungiyar Hamas, kuma yana daga cikin Sanatoci 12 da suka ki sanya hannu a wasikar da aka aikewa kungiyar kasashen Turai, dan sanya Hezbollah a matsayin kungiyar Yan Ta’adda.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.