Isa ga babban shafi
Amurka

Amurka ta fitar da sakamon binciken harin Kunduz

Ma’aikatar tsaron kasar Amurka ta fitar da sakamakon binciken harin sama da dakarun kasar suka kai bisa kuskure akan asibitin likitocin da basu da sanke na MSF a birnin Kunduz na Afghanistan da ya hallaka mutane 30

Sakataren tsaron Amurka Ash Carter
Sakataren tsaron Amurka Ash Carter REUTERS/Jonathan Ernst
Talla

Sakamakon binciken ya nuna cewar dakarun Amurkan sun kai harin ne bisa kuskure, inda kuma yanzu ma’aikatar tsaron kasar ta ce za ta dauki matakin ladabtar da sojojin da suka kai harin.

Janar John Campbell na kungiyar tsaro ta NATO ya ce tuni aka dakatar da sojojin da ke da hannu a harin daga aiki, ya kuma danganta wannan kuskuren da gajiya a bangaren sojojin ganin sun kwashe tsawon kwanaki biyar suna fafatawa da mayakan Taliban kafin su kaddamar da harin da ya abka wa asibitin.

A nata bangaren kungiyar likitoci ta MSF ta bukaci a tuhumi sojojin da ke da hannu a harin da laifin aikata laifukan yakin, yayin da ta rasa ma'aikata 14 a harin.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.