Isa ga babban shafi
Afghanistan-Nato-Amurka

Yan Taliban za su kadamar da sabin hare-hare kan gidajen talabijin

Kungiyar Taliban ta bayyana cewar zata kai hari kan manyan gidajen talabijin din kasar saboda abinda suka kira labaran karya da suke bayar wa cewar mayakan su na yiwa mata da yara fyade a Kunduz. 

Yan tawayen Taliban a Afganistan
Yan tawayen Taliban a Afganistan AFP PHOTO / Noorullah Shirzada
Talla

Kungiyar tace daga yanzu bata daukar gidan talabijin din Tolo da 1TV a matsayin kafofin yada labarai, sai dai a matsayin dandalin yada farfaganda.

Taliban tace daga yanzu babu wani ma’aikaci, ofishi ko kuma jami’an kafofin da zasu ragawa.

 Kungiyar Taliban da a baya ta sanar da harbo jirgin Sojin Amurka wanda ya yi hatsari a gabashin kasar Afghanistan, inda mutane 11 da ya hada da Sojojin kungiyar tsaro ta NATO suka rasa rayukansu, Zabihullah Mujahid ya sanar a shafin Twitter cewa mayakan kungiyar ne suka yi nasarar harbo jirgin mai dauke da mutane 11  a kusa da birnin Jalalabad.

Kanal Brian Tribus, wanda shima Sojan Amurka ne ya tabbatar da mutuwar mutanen dake cikin jirgin mai lamba C-130 wanda kuma ya gamu da hatsarin da misalin karfe 12 na daren da ya gabata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.