Isa ga babban shafi
Afghanistan

Taliban ta kafa tuta a Kunduz

Mayakan Kungiyar Taliban sun kaddamar da farmaki a lardin Arewacin birnin Kunduz dake kasar Afghanistan tare da kafa tutarsu a wani dandali.

An tura Jami'an tsaron Afghanistan domin fafatawa da Mayakan na Taliban
An tura Jami'an tsaron Afghanistan domin fafatawa da Mayakan na Taliban Reuters/路透社
Talla

Daruruwan mayakan kungiyar ne suka kai farmakin a safiyar yau a birnin na Kunduz wanda suka samu damar shiga daga hanyaoyi uku yayin da aka tura Jami’an 'Yan Sandan Afghanistan zuwa birnin domin fafatawa da Mayakan.

Wasu jami’an tsaro sun ce Mayakan sun yi nasarar fasa gidan yarin Kundiz, inda suka kubutar da 'yan uwansu, kana sun karbe ikon wani asibiti dake cikin birnin.

An dai samu hasarar rayuka da dama da suka hada da Jami'an 'Yan Sanda yayin da wasu kuwa suka jikkta.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.