Isa ga babban shafi
Amurka-Afghanistan

Amurka ta tsawaita zaman dakarunta a Afghanistan

Shugaban Amurka Barack Obama ya sanar da shirin kasar na ci gaba da barin sojoji 9,800 na Amurka a Afghanistan har zuwa shekara mai zuwa.

Shugaban kasar Amurka Barack Obama.
Shugaban kasar Amurka Barack Obama. REUTERS/Mike Segar
Talla

Daukan wannan matakin ya biyo bayan tattaunawar da aka kwashe watanni ana yi tsakanin shugabanin Amurka da Afghanistan.

Duk da cewa a baya Amurka ta sha yin alkawarin janyewa daga kasar, sai dai ci gaban hare-haren Taliban ya hana dakarun Amurka barin kasar.

Shugaba Obama ya kare matakin barin dakarun da cewa sojin Afghanistan sun kasa a fannin kare kan su da kasar inda ya ce suna bukatar taimakon Amurka.

A yayin da ya gana da dakarun kasar sa kuwa, ya basu kwarin gwiwa da cewa Amurka bata tura su cikin hadari ba face su taimakawa kasar da ke bukatar samarwa al’ummar ta zaman lafiya ta hanyar kawar da barazanar kungiyar Taliban mai tada kayar baya.

Sai dai tuni kakakin kungiyar Taliban, ya yi watsi da wannan shiri na Amurka, inda ya ce ba za su taba amincewa da hakan ba.

Rikici a kasar Afghanistan ya bar ke bayan kungiyar Taliban da ke rike da mulki a wanvan lokacin ta ki ta ki meka Osama Bin laden bayan harin ranar sha daya ga watan Satumba a Amurka .

Yanzu dai Amurka zata ci gaba da kasancewa acikin kasar ta Afghanistan har zuwa badi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.